Wasanni a Botswana

Wasanni a Botswana
sport in a geographic region (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara Botswana
Ƙasa Botswana
Wuri
Map
 22°12′S 23°42′E / 22.2°S 23.7°E / -22.2; 23.7

Wasanni a Botswana sun bambanta kuma suna da haɓaka sosai. Ko da yake, ƙwallon ƙafa, ƙwallon Raga da wasannin motsa jiki sun kasance mafi shaharar wasanni, yawancin lambobin wasanni, gami da wasan kurket, rugby, judo, ninkaya da wasan tennis suna aiki a fagen wasanni na ƙasa. Hukumar wasanni ta kasar Botswana (BNSC) tare da kwamitin wasannin Olympics na ƙasar Botswana (BNOC) da ma'aikatar matasa, wasanni da al'adu (MYSC) ne ke da alhakin kula da harkokin wasanni gaba daya a kasar. Bugu da ƙari, akwai sama da Hukumomin Wasanni na Ƙasa guda 30 da kuma ƙungiyoyin wasanni uku na makaranta [1]

Botswana tana gudanar da wasannin Botswana duk bayan shekara biyu, kuma ta karbi bakuncin wasannin matasan Afirka na shekarar 2014, Ƙungiyar Ayyuka ta Duniya akan Mata a Wasanni, da kuma gasar cin kofin duniya ta matasa ta ƙwallon ƙafa ta shekarar 2017 . Sun kuma nemi karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na matasa na bazara na shekarar 2022, amma sun sha kashi a hannun Dakar mai masaukin baki.

  1. Empty citation (help)

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search